Contact Information

Progress Radio 97.3 FM Gombe -Nigeria Plot 5988, Tumpure, Bauchi Road, Gombe Nigeria

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Kungiyar masu masana’antun samar da kayayyaki ta Najeriya ta koka kan yadda ake karawa mambobinta harajin shigo da kayayyaki ta gabar ruwa.

A cewar kungiyar wannan babbar matsala ce da ka iya durkusar da tattalin arzikin kasar, a don haka ya kamata gwamnati ta tashi tsaye wajen warware wannan matsala.

Yanzu haka dai masu masana’antun na biyan harajin dala 1500 kan kowacce kwantaina da ke shiga kasar daga kasashen waje, lamarin da a cewarsu ke kawo nakasu ga harkokinsu.

Alhaji Hassab Bello, shi ne shugaban hukumar da ke sanya ido kan shigar da kayayyaki ta gabar ruwa a jihar Legas, ya shaidawa manema labarai cewa ”Ba’ayi magana da su ba aka sanya wannan haraji, kuma hakan ya sa kayan da ake shiga da su kasar sun yi kasa sosai saboda daukar wannan mataki”.

Wannan dalili dai ya sa kungiyar masu masana’antun da kuma hadin guiwar cibiyar tallata haja ta jihar Legas ta gudanar da wani taro a jihar ta Legas, domin lalubo hanyar da ya kamata abi don shawo kan lamarin da suka ce yana kawowa harkokin kasuwancinsu koma baya, musamman a wannan lokaci na annobar korona.

A baya dai abin da ake karba a wurin masu masana’antu da ke shigar da kaya Najeriya ta ruwa bai wuce dala 150 zuwa dala 200 ba.

Ita ma hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya NPA ta bayyana goyon bayanta ga masu masana’antun, in da ta ce wani yunkuri ne na kawowa tattalin arzikin Najeriya koma baya.

Abubakar Garba ne ya wakilci hukumar a yayin taron da aka gudanar, ya kuma bayyanawa manema labarai cewa ”Lallai ya kamata a dakatar da wannan kari, ko don wannan hali da ake ciki na annobar korona.

 

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *