Gwamnonin jam’iyar APC sun jadadda kudurin su na dakile ta’addanci a shiyyar arewa maso gabashin kasan nan.
Sunyi alkawarin bada gudunmawan kudi ga harkar tsaro na jahohin da suke a yankin.
Shugaban kungiyar kana gwamanan jahar kebbi, Abubakar Bagudu, shine yayi wannan alkawarin yayin da ya ziyarci gwamnan jahar Borno Babagana Zulum domin yi masa jaje kan harin da yan ta’adda suka kai wa tawagarsa a karamar hukumar Baga.
Bagudu, wanda ya samu rakiyar gwamnan jahar jigawa Mohammed Badaru, yace kungiyar zata tara kudaden da ake bukata domin karfafa harkar tsaro a jahar Borno.
Yayin bayanin sa, badaru ya jinjinawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan nasarorin da aka samu a fagen yaki da ta’addanci.
Ya kuma yi kira na karin tallafin kudi da kuma karfafa harkar tsaro, domin dawo da zaman lafiya a jahar da kuma shiyyar arewa maso gabar baki daya.
Yayin mai da martani, gwamna Zulum wanda ya jinjinawa kungiyar na goyon bayan da ta bayar, yayi kira ga jami’an tsaro da su kara himma wajan dakile matsalar tsaro, inda ya kara da cewa, wadanda suka bazama suna bukatar su koma gidajen su.