Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce an samu nasarar ceto wani matashi da aka tsare shi a cikin gidansu tsawon shekara bakwai ba tare da ba shi damar fita ba.
Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Haruna Kiyawa, ya tabbatar wa manema labarai hakan a ranar Juma’a da safe.
A ranar Alhamis da yamma ne bidiyon da ke nuna yadda aka kuɓutar da yaron ya watsu kamar wutar daji a shafukan sada zumunta da muhawara a faɗin ƙasar.
A cikin bidiyon an ga yadda wasu mutane suka ɗauke shi suka saka shi cikin motar ‘yan sanda aka tafi da shi, yayin da wasu mutanen ke tattauna wa da shi yana nuna alamun farin ciki.
Sannan ƙasusuwan jikinsa duk sun fito, abin da ke nuna alamun yunwa da rashin lafiya.
Wannan lamari na zuwa ne a ranar da ‘yan sanda suka gurfanar da mahaifin yaron da aka ceto a Birnin Kebbi ranar Lahadi, wanda aka zargi matan ubansa da ɗaure shi a turken dabbobi tsawon shekara biyu.
A wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta fitar a ranar Juma’a bayan ta ce ta samu labari ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 11:15 na dare cewa wani mutum mai suna Aminu Farawa ya kulle ɗansa Ahmed Aminu mai shekara 30, a garejin motarsa tsawon shekara bakwai ba tare da ba shi isasshen abinci da kula da lafiyarsa ba.
Sanarwar ta ce daga nan sai tawagar runduar Operation Puff-Adder ta shiga lamarin. “An ceto mutumin aka kuma garzaya da shi Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammed Kano inda aka kwantar da shi. Kuma tuni an kama baban nasa,” in ji sanarwar.
Binciken farko-farko ya nuna cewa mahaifin Ahmed ya amsa laifinsa na kullen yaron tsawon shekara uku kan zarginsa da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.
Tuni dai kwamishinan ƴan sanda na jihar Kano Habu A. Sani ya bayar da umarnin mayar da batun Sashen Kula da Miyagun Laifuka na jihar SCID don yin ƙwaƙƙwaran bincike.